Connect with us

News

Matasan Kano sun yi zanga-zangar adawa da sace dalibai mata a Arewacin Najeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Daruruwan dalibai ne suka yi dandazo a Kano a yau Litinin don nuna adawa da yadda ake ci gaba da yin garkuwa da dalibai mata a manyan makarantun Arewacin Najeriya.

Daliban da suka yi tattaki a unguwar Rijiyar Zaki da ke cikin birnin Kano, sun bukaci a gaggauta ceto dalibai mata da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Gusau wato FUGUS kimanin watanni uku da suka gabata, da kuma wasu da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma, wato  FUDMA da sauransu na  Nasarawa State University, Keffi.

Advertisement

Hukumar KAROTA Ta  Gano Sabon Salon Da Direbobi Ke Yi Wajen Shigo Da Giya Jihar Kano

Kimanin dalibai mata 24 na FUGUS, da kuma dalibai mata hudu na FUDMA da ‘yan bindiga suka kama sama da watanni uku da suka gabata, har yanzu suna hannunsu kamar yanda Jaridar Daily Post ta ruwaito 

Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata an sako wasu dalibai bakwai na Jami’ar Tarayya da ke Lafia, FULAFIA, Jihar Nasarawa, wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su kwanaki hudu da suka gabata.

Advertisement

Amma har yanzu dalibai hudu da aka kama daga jami’ar jihar Nasarawa watannin baya suna hannunsu.

An gudanar da zanga-zangar ne a karkashin tutar ‘Arewa Mufarka’ ma’ana ‘Yan Arewa mu farka.

Advertisement

Da yake zantawa da manema labarai  jagoran zanga-zangar Sharfuddeen Bature, ya ce: “Mun dade muna kan lamarin. Yau kwana tamanin kenan da sace mutanen. Muna da ministoci a yankinmu – a Zamfara. Muna da mai ba da shawara kan harkokin tsaro, NSA, daga yankin mu.

“Muna bukatar dawowar wadannan ‘yan matan. Iyayen su suna cikin mawuyacin hali. Ba za mu daina yin haka ba har sai sun dawo da ‘yan matanmu”.

Advertisement

Masu zanga-zangar sun kuma yi Allah wadai da kisan kiyashin da jiragen yakin sojin Najeriya suka yi a baya-bayan nan sama da mutane 100 a yankin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending