Connect with us

News

Hukumar KAROTA Ta  Gano Sabon Salon Da Direbobi Ke Yi Wajen Shigo Da Giya Jihar Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta gano sabon salon da direbobi ke yi wajen shigo da Giya jihar Kano.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami, in yada labarai na Hukumar KAROTA Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa  ya turawa da Jaridar Inda Ranka

Ƙasashe biyar a gabashi da kudancin Afirka na fama da ɓarkewar cutar Anthrax

Sanarwar ta kara da cewa Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a yau lokacin da yake yaba kokarin jami’an Hukumar, wadanda suka sami nasarar gano dabarun da Direbobi ke yi wajen shigo da giyar jihar Kano.

Ya kara da cewa  an  sami nasarar cafke mota kirar Canta Mai lumbar FGE 407XB Wanda ta dakko giya fiye da kwalaba Dubu Hudu (K4600)

Advertisement

Jami’an da suka sami nasarar cafke motar sun bayyana cewa lokacin da suka tsayar da motar Direban ya bayyana musu cewa Itacan girki ya dakko, bayan da aka matsa bincike sai aka fahimci ba itacen ba ne Barasa ce a ciki

Shugaba Hukumar Engr. Faisal Mahmud Kabir ya ce bayan an kammala bincike za a mika Giyar ga Hukumar Hizba domin fadada bincike tare da daukar mataki na gaba.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending