News
Ƙasashe biyar a gabashi da kudancin Afirka na fama da ɓarkewar cutar Anthrax
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ƙasashe biyar a gabashi da kudancin Afirka na fama da ɓarkewar cutar anthrax, in ji hukumar lafiya ta duniya WHO a yankin Afirka.
Sama da mutane 1100 ne ake zargin sun kamu da cutar kuma mutane 20 ne suka muta a Kenya da Malawi da Uganda da Zambia da kuma Zimbabwe – tun farkon wannan shekara.
Ƙasar Zambia dai na fuskantar bullar cutar mafi girma tun shekara ta 2011, inda larduna 9 daga cikin 10 nata suka kamu da cutar.
Yayin da cutar ke yaɗuwa a cikin dabbobi a Malawi, ƙasar ta ba da rahoton bullar cutar ta farko da aka taɓa samu a bana.
Dakta Matshidiso Moeti, darektan hukumar ta WHO a Afirka ta ce tana tallafawa wajen ƙoƙarin yaƙi da ɓarkewar cutar a faɗin ƙasar.
Ta kara da cewa “Don kawo karshen wadannan barkewar dole ne mu karya tsarin kamuwa da cuta ta hanyar fara rigakafin cutar a dabbobi,” in ji ta.
Bbc ta ruwaito cewa masana kiwon lafiya, ana iya haifar da ɓarkewar cutar ta hanyar abubuwa da yawa, da suka haɗa da girgizar yanayi da ƙarancin abinci da rashin fahimta da kamuwa da cutar ta hanyar kula da naman dabbobin da suka kamu da cutar.
A wani labarin kuma Shugaban kasa, Bola Tinubu yana kan hanyar zuwa jihar Borno
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
