Connect with us

News

Shugaban kasa, Bola Tinubu yana kan hanyar zuwa jihar Borno

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana kan hanyar zuwa jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar domin halartar taron shekara-shekara na rundunar sojin ƙasar.

Wannan ce ziyara ta farko da ya kai yankin tun hawansa karagar mulki.

Babban Bankin Kasa CBN Ya yi Karin Haske Kan Karancin Takardun Kudi Na Naira

Cikin sanarwar da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin Najeriya, Brigediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, Shugaba Tinubu ne babban baƙo na musamman a taron.

A cewar sanarwar, bikin buɗe taron zai ƙunshi jawabi ga sojojin da ke aiki ƙarƙashin rundunar Haɗin Kai inda kuma zai yi rangadi kan asibitin sojoji a Maiduguri da kuma iza tubalin ginin hedikwatar shiyya ta bakwai kamr yanda Bbc ta ruwaito 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending