News
Jamhuriyar Nijar ta dakatar da haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Jamhuriyar Nijar ta dakatar da dukkan ayyukan haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa da ake kira (OIF) a taƙaice, a cewar shugabannin mulkin sojin ƙasar, yayin da take ƙara janye jiki daga tsohuwar uwargijiyar mulkin mallakarta.
Ƙungiyar mai wakilai 88 “a ko da yaushe Faransa na amfani da ita a matsayin wani makami wajen kare muradan Faransa”, a cewar wani mai magana da yawun shugabannin mulkin sojin kamar yadda ya bayyana a wani jawabi ta kafar talbijin ɗin ƙasar ranar Lahadi.
Aƙalla mutum 16 ne suka mutu a wani hari da aka kai ƙauyen Mushu da ke Jihar Filato
Tun cikin makon jiya ne, ƙungiyar ta OIF ta dakatar da mafi yawan ayyukan haɗin gwiwa da Nijar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, sai dai ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da harkokin da “kai tsaye za su amfani fararen hula da kuma waɗanda za su tallafa wajen mayar da Nijar kan mulkin dimokraɗiyya”.
Bbc ta ruwaito cewa Taken da ƙungiyar ke bayyanawa shi ne bunƙasa harshen Faransanci da tallafawa harkokin zaman lafiya da dimokraɗiyya da ƙarfafa gwiwar haɓaka ilmi da raya ƙasa a ƙasashe rainon Faransa a faɗin duniya, waɗanda da yawansu tsoffin ƙasashen Faransa ta yi wa mulkin mallaka ne.
A wani labarin kuma Aƙalla mutum 16 ne suka mutu a wani hari da aka kai ƙauyen Mushu da ke Jihar Filato
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
