News
NNPC ya Ƙaryata Raɗe-Raɗin Ƙarin Farashin Mai
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar gudanarwa na kamfanin Mai NNPC ta fito ƙaryata batun cewar farashin mai zai yi tashin Gwauron zabi.
Sanarwar ta fito ne daga bakin Babban jami’in sadarwa na Kamfanin Olufemi O.Somaye a jiya Laraba 3 ga watan Janairu 2024 Inda yake cewa ”Hukumar gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ta ƙaryata zancen da ke yawo na cewar kamfanin ta yi ƙarin farashin man fetur.”
Ɗangote ya koma matsayi na biyu na biloniyan da ya fi kowa ƙarfin arziki a Afrika.
Kamfanin na NNPC ya buƙaci yan Najeriya da su yi watsi da duk wata jita-jita da ba su da tushe balle makama kuma sun ba da tabbacin babu wani shiri na sake ƙara farashin Mai.
Haka kuma kamfanin ya shawarci masu ababen hawa da su daina fargaba saboda a halin yanzu akwai wadataccen Mai a ko ina a faɗin ƙasar.
A wani labarin kuma NNPC ya Ƙaryata Raɗe-Raɗin Ƙarin Farashin Mai
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
