News
Majalisar Wakila na nazari kan ƙudurin kafa ƙarin jami’o’i 47 a Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Akwai yiwuwar yawan jami’o’n gwamnatin tarayya kan iya kai wa 99 a ‘yan watanni masu zuwa, sakamakon wani kudiri da aka yi wa karatu na biyu a majalisar wakilan Najeriya.
Kudirin dai na son kafa ƙarin jami’o’i guda 47 a kasar, ƙari a kan guda 52 da kasar ke da su a yanzu haka.
Ɗaurin shekaru 14 ne hukuncin masu digirin bogi dan kwatano -Bulama Bukarti
Wannan kari ne a kan wasu kudurori guda 56 da majalisar ta yi wa karatun nabiyu domin kafa ƙarin Cibiyoyin kula da lafiya na gwamnatin taryya wato Federal Medical Centres a sassan ƙasar da dama.
Harwayau, majalisar na duba yiwuwar karin wasu kudurorin domin kafa wasu kwalejojin ilimi 32 da na koyan aikin noma 11 da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha guda biyar.
Bbc hausa ta ruwaito cewa Yanzu haka dai akwai manyan cibiyoyin kula da lafiya na gwamnatin tarayya guda 22 da kwalejojin ilimi guda 27 da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha guda 40, a faɗin Najeriya.
Waɗanda ake son kafawar yanzu sun hada da jami’o’in kimiyya da fasaha da na aikin gona da sufurin jirgin sama da kuma nazarin aikin injiniya da dai sauransu.
A wani labarin kuma Ɗaurin shekaru 14 ne hukuncin masu digirin bogi dan kwatano -Bulama Bukarti
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
