Connect with us

News

NiMet ta yi hasashen samun yanayin rana da buji daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a Najeriya 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun yanayin rana da buji daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a fadin kasar.

Hasashen yanayi na NiMet da aka fitar ranar Alhamis a Abuja ya yi hasashen za a yi wata ƙura a ranar Juma’a a yankin arewa.

Advertisement

Yadda Ƴan bindiga suka kai wa kauyukan da suka kasa biyan harajin naira miliyan 20

Daily Post ta ruwaito cewar ana sa ran zazzafar rana da hazo a yankin arewa ta tsakiya a duk tsawon lokacin hasashen.

Hukumar ta yi hasashen garuruwan da ke gabar teku a kudancin kasar da yiwuwar samun tsawa a sassan jihohin Ogun, Edo, Ondo, Legas, Delta, Ribas, da Bayelsa a lokutan rana da kuma yamma.

Advertisement

“A ranar Asabar, ana sa ran za a samu hazo kadan a arewa da yankin Arewa ta tsakiya lokacin.

“Akwai yiwuwar tsawa a ware a wasu sassan jihar Ondo, Ogun, jihar Legas, da  Riversbl, sai ku Edo, Akwa Ibom, Bayelsa, da Delta

Advertisement

An yi hasashen za a sami ƙura a yankin Arewa ta Tsakiya a lokacin hasashen.

A wani labarin kuma Yadda Ƴan bindiga suka kai wa kauyukan da suka kasa biyan harajin naira miliyan 20

Advertisement

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

Advertisement

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

Advertisement

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Advertisement

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending