News
Badakalar N585m: SERAP ta yi barazanar daukar matakin shari’a idan Tinubu ya kasa binciken Betta Edu
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Kungiyar SERAP mai fafutukar Kare Hakkokin Tattalin Arziki da tabbatar da demokradiyya ta yi barazanar gurfanar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a gaban kotu idan ya kasa binciki zargin biyan N585,189,500.00 a wani asusu na sirri da ministar harkokin jin kai da yaki da talauci, Betta Edu ta yi.
Kolawole Oluwadare, Mataimakin Darakta na SERAP ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
DAILY POST ta ruwaito cewa Betta Edu ta tabbatar da fitar da N585,189,500.00 da aka tanadar wa marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Legas, da Ogun a cikin asusun sirri.
Sai dai Edu ta dage cewa biyan kudin bai saba ka’ida ba.
A halin da ake ciki, SERAP ta ce matakin da ministar ta dauka ya sabawa bana na 7, sashe na 713 na kundin tsarin mulkin gwamnatin tarayya na shekarar 2009, wanda ya bayyana cewa, ‘Ba za a iya biyan kudin mutum a cikin asusun gwamnati ba, ko kuma a biya kudin al’umma a banki sirri.
Don haka, SERAP ta bukaci Tinubu da ya umarci Babban Lauyan Gwamatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Mista Lateef Fagbemi, da hukumomin da suka dace na yaki da cin hanci da rashawa da su gaggauta gudanar da bincike.
Ku tuna cewa Akanta-Janar na Tarayya, Oluwatoyin Madein, ya ce Edu bai kamata ya sanya N585,198,500.00 a cikin asusun sirri ba.
