Connect with us

News

An kama wani matashi da ake zargi da laifin daba wa mahaifinsa wuka har lahira a Kano

Published

on

DAGA USMAN IBRAHIM BELLO 

 

Advertisement

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC reshen jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 25 mai suna Alkasim Ya’u da laifin daba wa mahaifinsa wuka har lahira a Tudun Yola ‘C’ da ke karamar hukumar Gwale a jihar.

Kwamandan hukumar NSCDC, Mohammed Falala ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasaa NAN ta wayar tarho a Kano yau Lahadi.

Advertisement

Badakalar N585m: SERAP ta yi barazanar daukar matakin shari’a idan Tinubu ya kasa binciken Betta Edu

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 1:30 na rana a gidan Alhaji Salisu Bala.

“Mahaifin marigayin, Alhaji Ya’u Mohammed, ya kawo dansa mai tabin hankali, Alkasim Ya’u, zuwa asibitin mahaukata na Dawanau, domin neman lafiya, inda suka nemi ganin likita a ranar Asabar, 6 ga watan Janairu,” inji shi.

Advertisement

Ya bayyana cewa, maimakon ya koma Katsina, marigayin ya yanke shawarar kwana a gidan dan uwansa.

“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa Alkasim ya kamu da tabin hankali ne sakamakon yadda yake gudanar da ayyukan ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Advertisement

“A lokacin da suka isa Tudun Yola, dan mara lafiyar ya dauki wani abu mai kaifi ya raunata mahaifin sa , har sai da jami’an NSCDC da ke yankin suka shiga tsakani suka kai wanda aka kashen asibiti suka kama wanda ake zargin,” inji shi.

Ya ce ‘yan uwa suna shirye-shiryen mayar da gawar Katsina domin yi mata jana’iza, yayin da aka mika wanda ake zargin  ga ofishin ‘yan sanda na Rijiyar Zaki domin ci gaba da bincike.

Advertisement

A wani labarin kuma Badakalar N585m: SERAP ta yi barazanar daukar matakin shari’a idan Tinubu ya kasa binciken Betta Edu

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a ka

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending