News
Kisan Nafi’u: Kotu Ta Dage Shari’ar Hafsat Chuchu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kotun Majisatare a Kano ta dage shari’ar matar auren nan Hafsat Surajo (Hafsat Chuchu), wadda ake zargin ta yi wa wani matashi mai suna Nafiu Hafizu kisan gilla.
A ranar Litinin ne kotun da ke zamanta a unguwar Yankaba da dage zamanta zuwa ranar 18 ga watan nan na Janairu domin sauraron bukatar belin Hafsat Chuchu kan zargin kisan matashin, wanda abokinta ne.
Gwamnan Kogi Yahaya Bello Ya Kori Sarakunan Gargajiya Hudu, Ya Yi Sabon Nadi
Mai Shari’a Hadiza Abdulrahman, ta kuma ta ba da umarnin mayar da wadana ake zargin gidan yari ne bayan lauyoyinsu Rabiu Sidi da Rabiu Abdullahi sun nemi a ba da belinsu.
An gurfanar da Hafsat Chuchu ne a tare da mijinta Dayyabu Abdullahi da wasu mutum biyu da suka hada da malamain da ya yi wa gawar Nafiu wanka da kuma mai gadin gidan ma’auaratan.
Aminiya ta ruwaito cewa Kotun ta ba da umarnin a mayar da wadanda ake zargi gidan yari zuwa ranar zama na gaba.
An gurfanar da Hafsat kan zargin aikata kisa da kuma yunkurin kashe kanta, zargin da ta musa a gaban kotu.
Da farko, a hannun ’yan sanda ta amsa cewa ita ce ta kashe Nafiu ta hanyar sossoka masa wuka saboda ya hana ta ta kashe kanta.
Sauran mutum ukun kuma ana zargin su ne da hada baki wajen aikata laifi, boye laifi da kuma ba da shaidar karya.
A ranar 27 ga Disamba, 2023 ne aka fara gurafnar da su, inda Mai Shari’a Hadiza Abdulrahman ta sa a tsare su a gidan yari kafin zama na gaba.
A wani labarin kuma Gwamnan Kogi Yahaya Bello Ya Kori Sarakunan Gargajiya Hudu, Ya Yi Sabon Nadi
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
