News
Kotun sojojin Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarni a saki dan Bazoum
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Wata kotun soji a Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarni a saki Salem, wato dan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum Salem.
An yi wa Salem, mai shekara 23, daurin-talala tare da mahaifansa a gidan shugaban kasa da ke Yamai tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
Guinea ta danƙara wa Super Eagles kwallaye biyu a raga, bayan kurin lallasa Al-Gharib 12-0 da ta yi
Juyin mulkin, wanda shi ne na takwas da sojoji suka yi a Yammaci da Tsakiyar Afirka tun daga 2020, ya jawo wa kasar bakin-jini, har ya kai ga kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta sanya mata takunkumi yayin da kuma kasashen duniya suke ta kiraye-kiraye a Bazoum tare da mika mulki ga gwamnatin dimokuradiyya.
Kotun ba ta yi bayani game da makomar Bazoum da mai dakinsa ba.
A wani labarin kuma An ci tarar Kano Pillars Naira miliyan 10
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
