Connect with us

News

Badakalar Kudi: EFCC Ta Kwace Fasfo Din Betta Edu Da Sadiya Farouk Domin Hana Su Guduwa.

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

A halin da ake ciki, an kuma kama fasfo din tsohuwar ministar Sadiya Umar-Farouk a wani bangare na Sharuddan belin wanda daga bisani aka sake ta da yammacin ranar Litinin.

Advertisement

Har Ila Yau Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta kwace fasfo din tsohuwar ministar jin kai da yaki da fatara da fatara, Betta Edu domin hana su mutanen biyu ficewa daga kasar nan, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan zambar da suka aikata.

Kotun Koli Zata Yanke Hukumci Mako Mai Zuwa Kan Zaben Jihar Filato

Shugaba Bola Tinubu ne ya dakatar da Ministar Jin Kai Sakamakon Zargin zamba da ku’din ma’aikatar ta jinkai.

Advertisement

A wani labarin kuma Kotun Koli Zata Yanke Hukumci Mako Mai Zuwa Kan Zaben Jihar Filato

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending