Connect with us

News

Kotun Koli Zata Yanke Hukumci Mako Mai Zuwa Kan Zaben Jihar Filato

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Kotun kolin Najeriya ta jingine hukunci a karar da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya shigar inda ya bukaci ta tabbatar da zabensa.

Gwamnan ya yi zargin cewa kotun daukaka kara ba ta yi masa adalci ba, kan matakin da ta dauka na soke zaben nasa.

Advertisement

Mutum 1,227 Sun Kamu Da Zazzabin Lassa Yayin Da Cutar Ta Yi Ajalin Mutum 219 A Najeriya A Shekarar 2023.

A ranar 19 ga watan Nuwamba Kotun daukaka kara ta kori gwamnan tare da bayyana ‘dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nentawe Yilwatda a matsayin wanda ya lashe zaben.

Muryar Amurka ta ruwaito cewa Gwamna Caleb Mutfwang, da bai amince da hukuncin kotun daukaka karar ba, ya bukaci kotun kolin ta ayyana shi a matsayin gwamna.

Advertisement

Mutfwang ta bakin lauyansa Kanu Agabi (SAN) ya ce batu guda daya ne kotun daukaka kara ta duba, daga cikin ababe takwas da suka gabatar a gabanta. Ya ce hukuncin kotun daukaka karar ya saba wa umurnin kotun koli, cewa ya kamata kotuna na tsakiya su duba dukkan batutuwan da aka gabatar a gabansu.

A lokacin sauraron karar a jiya Talata, rukunin mutane biyar na Kotun kolin karkashin shugabancin mai shara’a John Okoro sun saurari muhawara tsakanin dukkan bangarorin lauyoyin dake cikin shari’ar.

Advertisement

Bayan jayayya mai tsanani tsakanin lauyan Caleb Mutfwang, Kanu Agabi, da lauyan Nentawe Yilwatda, J.O Olatoke, kotun kolin ta ce za a sanar da ranar hukunci ga wadanda suke cikin karar. Amma kafin jingine hukuncin, Kotun kolin ta gabatar da tambayoyi biyu masu muhimmanci game da ko kotun sauraren kararrakin zabe tana da ikon saurarar batutuwan da suka shafi jami’iyya.

Kotun kolin ta ayyana ranar 16 ga Janairu a matsayin ranar da zata yanke hukunci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending