Connect with us

News

KANO: Kotu ta daure matashin da ya kashe limami a gidan gyara hali

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Kotun majistare a jihar Kano ta daure wani matashi Yusuf Haruna mai shekara 18 a gidan gyaran hali bisa laifin kashe limami Sani Mohammed da wuka.

Advertisement

An gurfanar da Haruna mazaunin kwatas din Tudun Nufawa a gaban kotun bisa laifin kisa.

Wata Sabuwa: Ƙungiyar Ƙwadago ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnati

Lauyan da ta shigar da karan Fatima Ado-Ahmad ta ce wani Musa Inusa ne ya sanar da ‘yan sanda kisan da Haruna ya yi a ofishin su dake Jakarta ranar 31 ga Disemba.

Advertisement

Ta ce a wannan ranar da misalin karfe 7 na yamma Haruna ya daba wa limami wuka inda hakan ya yi ajalin sa.

“An yi gaggawar kai shi asibiti amma likita ya tabbatar cewa ya mutu.

Advertisement

Sai dai kuma Haruna ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi yayin zaman kotun.

Alkalin kotun Binta Galadanchi ta yanke hukuncin daure Haruna a gidan gyara hali sannan za a ci gaba da shari’a ranar 31 ga Janairu.

Advertisement

A wani labarin kuma Wata Sabuwa: Ƙungiyar Ƙwadago ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending