Connect with us

News

Yanzu haka dai hankulan ƴan jihar kano ya koma kacokan kan hukuncin kotun ƙoli da zata yanke a ranar juma’a

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Yanzu haka dai hankulan ƴan jihar kano ya koma kacokan kan hukuncin kotun ƙoli da zata ya ke a ranar juma’a kan ko Gawuna is coming ya tabba ko kuma Abba is staying.

Advertisement

Tuni dai Kotun koli ta sa da yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf na NNPP da kuma Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

KANO: Kotu ta daure matashin da ya kashe limami a gidan gyara hali

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar Yanke Hukuncin zaben gwamnan Jihar kano

Advertisement

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Advertisement

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda  yanke ranar Juma’a 12 ga watan Junairu 2024, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Advertisement

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending