News
KHETFUND Ta Taimaka wa Kwalejin Kimiyya da Fasahar Lafiya Da Sama Da N4m
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na samar da karin kudade ga bangaren kiwon lafiya, Asusun Kula da Lafiya na Jihar Kano ya mika tallafin kudade ga Kwalejin Kimiyya da Fasahar Kiwon Lafiya da kudade domin sayen kayayyakin ofis.
Baya ga asibitoci, su ma cibiyoyin ilimin kiwon lafiya na cikin rukunin da za su rinka amfana da tallafin da Hukumar ke bayarwa kamar yadda aka bayyana a cikin kundin jagorar masu cin gajiyar tallafin Hukumar.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.
Sanarwar ta kara da cewa a burinta na samun wurin aiki mai yanayin da ya dace don aiwatar da ayyukan gudanarwa, Kwalejin ta bukaci KHETFUND ta tallafa mata da kudade don gyara ofisoshinta domin gudanar da ayyukanta na yau da kullum yadda ya kamata, inda Hukumar ta bai wa Kwalejin Naira 4,497,900 bisa sahalewar Mai Girma Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Domin tabbatar da yin amfani da tallafin da KHETFUND ke bayarwa ga wadanda ke amfana, Sakatariyar Zartarwar KHETFUND, Dakta Fatima Usman Zahradeen, ta jagoranci tawagar sa ido zuwa Kwalejin domin duba kayayyakin da aka sayo domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Da take jawabi, Dakta Fatima ta bukaci mahukuntan Kwalejin da su tabbatar sun yi amfani da kayan da aka saya bisa manufar da aka sayo su.
Ta yi nuni da cewa, an kafa KHETFUND ne domin ta rinka samar da karin tallafin kudi ga cibiyoyi da makarantun lafiya a kan ayyuka masu ma’ana da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’ummar jihar.
Dakta Fatima ta yi amfani da wannan damar wajen yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kishinsa na daukaka tsarin kiwon lafiya, inda cikin farin ciki ta bayyana cewa sadaukarwar da mai girma Gwamna ya yi na samar da sakamako mai kyau da karara kowa na ganin sauye-sauyen da aka samu a jihar.
Ta kuma yabawa Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf bisa yadda yake ci gaba da ba da jagoranci, shawarwari da goyon baya ga KHETFUND.
Da yake jawabi a lokacin da yake karbar tawagar, Mataimakin Shugaban Kwalejin, Kwamared Garba Haruna Abubakar ya gode wa Sakatariyar Zartarwar da jami’an hukumarta wajen ba su kudaden domin sayo kayayyakin ofis, inda ya yi alkawarin amfani da su ta hanyar da ta dace.
Ya jaddada cewa, kayan aikin za taimaka wajen samar da yanayi mai kyau ga ma’aikatan gudanarwa don gudanar da ayyukansu sosai wadanda daga karshe zai share hanya don samun saukin koyarwa a Kwalejin ta yadda za a samar da kwararrun daliban da za su bayar da tasu gudummawar wajen inganta aiki idan an dauke su aikin gwamnati.
Kayayyakin da aka saya sun haɗa da kwamfutoci, jannareto, firintoci, akwatunan ajiyar fayil, na’urorin daidaita wutar lantarki, da sauransu.
