Connect with us

News

Kashi 81 cikin ɗari na ma’aikatan Najeriya ba su da amfani’

Published

on

Shugaban kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa na manufofi da tsare-tsaren kuɗi da sauye-sauye a haraji, Taiwo Oyedele.

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kusan kashi 81 cikin ɗari na ma’aikatan Najeriya ba sa wani ɓangare da ke samar da cigaba ga tattalin arziƙin ƙasar, in ji shugaban kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa na manufofi da tsare-tsaren kuɗi da sauye-sauye a haraji, Taiwo Oyedele.

Advertisement

Oyedele ya ce duk da cewa yawan marassa aiki a Najeriya kaɗan ne inda yake kashi 4.2 cikin ɗari, yawancin ‘yan ƙasar masu aiki ba su da wani amfani na ƙwarai ga tattalin arziƙin ƙasar.

Gwamnatin Jihar Kano Da ICPC Sun Kulla Alakar Aiki Kan Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Mista Oyedele ya ce Najeriya na mataki ɗaya ne da Birtaniya wajen yawan kashin marassa aikin yi wato 4.2 cikin ɗari, kuma abin da ya sa kenan har yanzu Najeriya ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi talauci a duniya.

Advertisement

Ya ce akwai mutum sama da miliyan 113 da ke cikin fatara a Najeriya a shekara ta 2022, kuma yana ganin shakka babu yawan a yanzu ya fi haka domin a lokacin ba a janye tallafin mai ba da kuma daidaita farashin canjin dala.

Shugaban kwamitin na magana ne a wajen taron ƙoli na kasuwanci da zuba jari na Afirka a yau Alhamis, a Lagos.

Advertisement

Oyedele ya ce kasancewar Najeriya ba za ta iya sauya alƙibilar tattalin arziin duniya ba, amma yin sauye-sauye a manufofinta ka iya taimaka wa halin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending