Connect with us

News

Fa’idoji da Falalar Salatin Annabi (SAW) Gada 25

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

TAMBAYA: Salatin Annabi guda nawa ne?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Advertisement

Salatin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Salama, daya ne daga cikin manyan Ibadu, kuma addu’a ce daga cikin addu’o’i masu amfani duniya da lahira, kuma yana daga cikin abubuwan da ke nuna cikkakiyar soyayya da girmamawa ga Annabi SAW, kuma hakki ne daga cikin hakkokan sa Sallallahu Alaihi wa Sallam.

Wajibi ne musulmi dan adam ya yawaita yin salati domin Fa’idoji da Falalar Salatin Annabi (SAW) nasa adace ranar gobe kiyama

An ruwaito sigogin salatin Annabi SAW, da yawa a cikin ingatattun Hadisan sa, Amma mafi daraja daga cikin salatin Annabi SAW, shi ne sigar da Annabi ya yayar da sahabban sa, wanda Imamul Mukhari da Muslim suka ruwaito kamar haka:

Advertisement

«اللهمَّ صلِّ على محمَّد وعلى آل محمَّد، كما صليتَ على إبراهيم وعلى آل

إبراهيم؛ إنَّك حميدٌ مجيد. اللهمَّ بارِك على محمَّد وعلى آل محمَّد،

Advertisement

كما باركتَ على إبراهيم وعلى آل إبراهيم؛ إنَّك حميدٌ مجيد».

البخاري (3370 / (مسلم (406)

Advertisement

Imamun Nawawi ya hada sigogin salatan a cikin wanna sigar da wasu malamai ke ganin girman darajar sa:

اللهم صل على محمد عبدك ورسولك النبي الأمي وعلى آل محمد وأزواجه وذريته

Advertisement

كما صليت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم وبارك على محمد وعلى آل محمد

وأزواجه وذريته كما باركت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم في العالمين إنك

Advertisement

حميد مجيد.

Babu laifi mutum ya takaita salati kamar Allahuma Sali Ala Muhammad wala Ali Muhammad, ko Sallallahu Alaihi wa Sallam da sauran gajerun lafuzzan salati.

Advertisement

Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salama, wajibi ne akan dukkan musulmi. An wajabta salatin ne ba tare da bada lokacin yinsa ba. Wato, ana son bawa ya yawaita yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam.

Hadisai sun ingata cewa duk wanda baya yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam, to, an turmuza hancinsa cikin wuta. A wani kaolin kuwa akace ya kuskure hanyan Al-Jannah.

Advertisement

GURAREN DA AKESON YIN SALATIN SALLALLAHU ALAIHI WA SALAM

1) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam bayan tahiyar karshe a cikin Sallah.

Advertisement

2) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam duk lokacin da aka ambaci sunan sa ko aka rubuta shi.

3) Anyi umurnin yawaita Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam duk ranar juma’a.

Advertisement

4) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam yayin shiga ko fita masallaci.

5) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam bayan tahiyar karshe a cikin Sallah.

Advertisement

6) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam bayan tahir karshe a cikin Sallah.

7) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam bayan kiran Sallah.

Advertisement

8) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam lokacin hudubar juma’a ko makamantan ta.

9) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam kafin addu’a.

Advertisement

10) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam a duk inda mutum ya zauna kafin ya tashi a gurin.

FA’IDODIN/FALALAN SALATIN ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WA SALAM

Advertisement

 

Salatin Annabi SAW wata irin ibadah ce wacce babu irinta acikin dukkan ibadun da Mumini zai iya yi da harshensa. Tana kunshe da falala wacce ‘Dan Adam ba zai san iyakarta ba. Domin ita wata babbar hanya ce wacce take nuna jin Ƙai irin na Allah ga bayinsa.

Advertisement

 

Malamai kamar Muhammad Miftah Bn Salih da Ibnul Qayyim Al-Jawziyyah sun kawo fa’idodin Salatin Annabi SAW da dama wanda ZAUREN FIQHU ta tsamo kadan daga ciki kamar haka:

Advertisement

 

1. Cika umurnin Allah ne tunda shi ya umurci Muminai suyi salati ga wannan Annabin mai girma SAW.

Advertisement

 

2. Yin Muwafaƙah da Allah, wato yin irin abinda Allah ma yana yinsa.

Advertisement

 

3. Yin Muwafaƙah da Mala’ikunsa, tunda su ma suna yin Salati agareshi SAW.

Advertisement

 

4. Ana daukaka darajar mutum har sau goma, saboda salati guda ‘daya Tal wanda yayi ma Annabi SAW.

Advertisement

 

5. Za’a rubuta maka kyawawan lada har guda goma, Ta dalilin Salati guda ‘daya tal!.

Advertisement

 

6. Allah da kansa zai maka salatai guda goma irin nasa.

Advertisement

 

7. Za’a kankare maka laifuka guda goma.

Advertisement

 

8. Za’a amshi dukkan abinda ka roƙa bayan Salati ga Manzon Allah SAW.

Advertisement

 

9. Dalili ne na samun ceton Manzon Allah SAW idan kayi salatin shi kadai ko kuma ka hada da neman Waseelah ga Manzon Allah SAW.

Advertisement

 

10. Dalilin samun gafara ne daga Allah.

Advertisement

 

11. Shi Salatin Annabi SAW babbar hanya ce ta samun isarwar Allah gareka akan dukkan abinda ya dameka (wato Allah zai share maka hawayenka).

Advertisement

 

12. Salatin Annabi SAW hanya ce ta samun kusanci ga Manzon Allah SAW aranar Alqiyamah.

Advertisement

 

13. Idan kayi salati agareshi SAW to Allah zai baka ladan wanda yayi sadaqah. (Musamman ga Matalauta).

Advertisement

 

14. Hanya ce ta samun biyan bukatu cikin Sauki in sha Allahu.

Advertisement

 

15. Hanya ce ta samun Salatin Mala’iku agareka da zarar kayi masa salati.

Advertisement

 

16. Hanya ce ta samun tsarkakuwar zuciyar mai yin salatin.

Advertisement

 

17. Hanya ce ta samun bisharar samun Aljannah agareka tun kafin mutuwarka.

Advertisement

 

18. Hanya ce ta samun tsira daga tashe-tashen hankulan ranar Alkiyamah.

Advertisement

 

19. Hanya ce ta samun mayar da salati da sallama agareka daga Annabi SAW.

Advertisement

 

20. Hanya ce ta samun tunawa da abinda ka manta (Wato idan ka manta da wani abu, da zarar kayi ma Annabi salati sai kaji ka tuno da abun).

Advertisement

 

21. Hanya ce ta samun kamshin wajen Zama, kuma duk wajen zaman da akayi ma Annabi salati, ba zai zama abin nadama ga Ma’abotansa ba, a ranar Alkiyamah.

Advertisement

 

22. Ta dalilin yin salati agareshi za’a cire sunanka daga layin Marowata a wajen Allah.

Advertisement

 

23. Ita hanyar tsira ne ga mai yinta, Domin Allah zai kirashi da bawansa.

Advertisement

 

24. Ita hanya ce ta samun kuɓuta daga turmuzuwar hanci ga wanda bai yi salati agareshi ba, duk sanda aka ambaceshi.

Advertisement

 

25. Salatin Annabi (saw) yana sanya mai yinsa akan Tafarkin shiga Aljannah.

Advertisement

 

Salati da aminci su tabbata agareka Ya Abal Qasimi, gwargwadon darajarka da matsayinka awajen Ubangijinka.

Advertisement

 

Albarkacin wannan salatin ya Allah ka zaunar da kasammu lafiya kuma tabbatar damu bisa tafarkinka madaidaici, tare da ‘Ya’yanmu da dukkan al-ummar musulmi. Amin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending