Connect with us

News

Yan Sanda Sun Cika Hannu Da Mahadi Shehu A Abuja Kan Zargin Damfarar Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rahotanni sun tabbatar da cewar hukumar Yansanda ta kasa reshen babban Birnin Tarayya Abuja, ta cika hannu da Wani attajirin Dan kasuwa Mamallakin gine-gine Dialogue, Malam Mahadi Shehu.

Advertisement

Kamen ya biyo bayan korafin da tsohon Ministan Sharia ta kasa Abubakar Malami ya shigar na tsargin Mahadi Shehu da kokarin yi masa damfarar kudade da yawan su ya Kai nera miliyan 500 ta manhajar Whatsapp.

Najeriya ta yi wajerod da Afirka ta Kudu a bugun fenareti, kuma ta kai wasan ƙarshe.

Tukumar ta ce Mahadi Shehu yayi kokarin wanke Abubakar Malami ko Damfarar sa ta hanyar da bata dace ba.

Advertisement

Sanarwar kamen Mahadi Shehu, na kunshe a cikin wata takardar manema Labarai da Lauyoyin sa suka rabewa manema Labarai, Kuma sanarwar tace Lauyoyin na kokarin karbar belin sa tare da karyata mu’amalar kudade dake tsakanin sa da Malami.

Wannan Kamen da aka yiwa Mahadi Shehu, ya zo kwanaki kadan bayan daya chachchaki tsofaffin jami’an tsohuwar Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari data gabata kan wasu batutuwa ciki har da almundahana.

Advertisement

Kafin yanzu rahotanni sun ce Mahadi Shehu yayi kaurin suna wace Sukar Gwamnati Mai ci ta APC hanyoyi mabanbanta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending