News
Tallafin Kayan Aikin Asibiti: Kayan Asibiti Sunzo Akan Lokaci – DR NAGODA
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Sakataren zartarwa na hukumar kula da asibitocin jihar Kano Dakta Mansur Mudi Nagoda ya bayyana jin dadinsa kan tallafin kayan aikin asibiti da kamfanin Minjirya Health Services Limited ya bayar.
Da yake gabatar da kayyakin a madadin Manajan Daraktan Kamfanin Mustapha Hussain Falaki, Nura Adamu Kibiya ya bayyana cewa tallafin na daga cikin tallafin da kamfanin ke bayarwa domin yaba da kokarin gwamnati na farfado da harkar lafiya a jihar.
Raɗaɗin Tsadar Rayuwa Ya Harzuƙa Ƙungiyoyin Ƙwadago, Sun Bai Wa Gwamnati Wa’adin Shiga Yajin Aiki
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwar da Jami ar yada labarin ta hukumar Samira Suleiman ta turawa da Jaridar Inda Ranka
Sanarwar ta kara da cewa Kayayyakin na miliyoyin naira da aka bayar sun hada da, na’uran dialysis, iskar oxygen, incubator, dakin gwaje-gwajen iska mai zafi, dakin gwaje-gwaje autoclave.

Haka kuma a ranar 6 ga Oktoba, 2023, wannan kamfani ya ba da gudummawar ɗaya kowace na’urar incubator, tanda mai zafi da firjin dakin gwaje-gwaje ga asibitin cututtukan da aka fi sani da IHD.
Da yake karbar kayayyakin, Dokta Nagoda ya ce kayayyakin sun zo daidai da yaka mata saboda karuwar bukatar amfani da su. Injin dialysis inda nan take aka baiwa Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase a daidai lokacin da cibiyar ke neman karin na’ura domin biyan bukatun jama’a.

A nasa jawabin, Hon. Kwamishinan ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf ya godewa Manajan Daraktan bisa wannan karimcinsa inda ya kara da cewa kayayyakin da aka bayar musamman na’urorin dialysis guda 2 da kudinsu ya kai miliyan 60 sun kawo saukin matsalar a asibitin nasarawa.
