News
Ɗalibin Shekarar ƙarshe Jami’ar AUA ya kashe abokiyar karatunsa akan iPhone
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wani dalibin Jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba wadda akafisani da (AAUA) Olubodun Sanni Mai kimanin shekaru 21, an kama shi bisa zargin kashe abokin karatun,sa Mai suna Mis Adekunle Adebisi Ifeoluwa
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa An tsinci gawar Miss Adekunle a ranar 2 ga Fabrairu, 2024 a cikin wani gidan haya dake kusa da harabar makarantar.
Ɗalibin Shekarar ƙarshe Jami’ar AUA ya kashe abokiyar karatunsa akan iPhone
Ana zargin Sanni da kashe abokiyar karatunsa nasa ne har lahira Domin ya mallaki wayar ta Mai kirar iPhone X
Dalibin ya kasance Daya daga cikin dalibin dake matakin aji na 300 dake karantar fannin tattalin arziki wato economics.
Kwamishinan ‘yan sandan Ondo, Abayomi Peter Oladipo, wanda ya yi magana a lokacin da yake gabatar da wasu mutane da ake zargin ya ce ‘yan sandan sun gano cewa wayar da ta mutu ta bace bayan kisan.
Abayomi ya bayyana cewa, ‘yan sanda sunyi amfani da fasahar zamani sun gano wayar ga wani matashi mai suna Sanni mai shekaru 21 wanda kuma makwabci ne ga marigayin a cikin dakin kwanan dalibai.
Ya ce Wayar da aka gano ta kai ga yiwa wanda ake zargin tambayoyi wanda ya ba da cikakken bayani game da abin da ya faru a cikin sanarwar da ya yi na bayani
Ya ce za a gurfanar da Sanni gaban kotu a karshen sashin laifuffukan kinsan Kai
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
