Connect with us

News

Buhari, Emefiele da Boss Mustapha ne suka ce a kamfaci Naira biliyan 2.9. —Mai bada shaida a kotu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Mai bayar da shaidar da mai gabatar da ƙara ya gabatar wa Babbar Kotun FCT Abuja, ya bayyana wa Mai Shari’a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta bada umarni aka kamfaci Naira biliyan 2 da Naira miliyan 900 domin biyan masu sa-ido kan zaɓen 2023.

Wanda ta bada wannan shaida ita ce Onyeka Ogau, tsohuwar Mai Kula da Reshen CBN, wadda yi wannan bayani a lokacin da ta ke bada shaida a shari’ar da ake ci gaba da gudanarwa ta tuhumar tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Yunkurin Juyin Mulki: Yau Shekaru 48 Da Kisan Janar Murtala Ramat Muhammad 

Ogau ya ce ya karɓi umarnin ya biya Dala miliyan 6.23 a ranar 8 ga Janairu, 2023, kamar yadda wani bayanin da Hukumar EFCC ta fitar, wanda ya labarta yadda zaman kotun ya wakana a ranar Litinin.

Mai bayar da shaidar dai lauyan EFCC ne ya gabatar da shi, wato lauya Oyedepo Rotimi, SAN a gaban Mai Shari’a Hamza Muazu.

Advertisement

Ogau ya ci gaba da yi wa kotu bayanin cewa an rubuto masa takardar umarni daga na gaba da shi, wadda a Turance ake kira ‘memo’, an haɗa takardar da kwafen bada umarnin cirar kuɗaɗen da Shugaba Muhammadu Buhari, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kuma Godwin Emefiele.

Ɗaya daga cikin umarnin ya ce a biya Dala miliyan 6.23 ga wani ma’aikacin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

An cire kuɗaɗen cikin Janairu, 2023, lokacin farashin Dala 1 a hannun Gwamnatin Tarayya Naira 461 ce. Hakan ya nuna an cire adadin Naira biliyan 2.9 kenan.

Premium Times ta ruwaito cewa a zaman sauraren bada shaidar da Ogau ya yi, bai ambaci sunan ma’aikacin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ɗin da aka damƙa wa kuɗaɗen ba.

Amma dai bayanan da aka bayar dalla-dalla sun nuna an cire kuɗaɗen a ƙarƙashin Godwin Emefiele.

“Ya Mai Shari’a. Dama a bisa tsari da ƙa’ida, duk wani umarnin a cire kuɗaɗe ana turo shi ne ta ofishi na, wato ofisoshin kwanturola na reshen banki.

Advertisement

“To a waccan ranar, Ya Mai Shari’a, an turo min kwafe-kwafen umarnin na biya kuɗaɗen har Dala 6,230,000. Kuma aka ce na biya kuɗaɗen ga wani ma’aikacin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya. Kuma sanarwar da umarnin na ɗauke da suna da hoton ID katin wanda zan bai wa kuɗin,” inji Ogau.

Ya ci gaba da shaida wa alƙali cewa kuma cewa aka yi na biya kuɗin kash, da Naira ta adadin Dala 6,230,000 ɗin da ke a rubuce.”

“A cikin ‘memo’ ɗin an rubuto cewa za a maida kuɗaɗen a cikin watanni ukun tsakiyar shekarar 2023 daga Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta Tarayya.”

Gurungunɗumar Biyan Kuɗaɗen ‘Masu Sa-ido Kan Zaɓe’:

Ogau ya shaida wa kotu cewa CBN ta biya kuɗaɗen a ranar 8 ga Afrilu, 2023, fiye da wata ɗaya bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa.

Ogau duk ya gabatar wa kotu kwafen takardun umarnin da aka bayar na biyan kuɗaɗen.

Advertisement

 

Za a ci gaba da sauraren shari’ar a ranar 13 ga Fabrairu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending