News
Yunkurin Juyin Mulki: Yau Shekaru 48 Da Kisan Janar Murtala Ramat Muhammad
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
GCFR Janar Murtala Ramat Muhammad, tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, wanda ya jagoranci hambarar da mulkin soja na janar Johnson Aguiyi-Ironsi a shekarar 1966, ya mulki Nijeriya daga watan Yulin 1975 har zuwa lokacin da aka kashe shi a ranar 13 ga Fabrairun 1976.
Ramat, Janar ne da ya yi fice a lokacin yakin basasa na Biafra.
Bayan Makonni Shida Da Aure: Amarya ta yi wa angonta yankan rago
An haife shi a Kano, 8 Nuwamba 1938 ya fara aikin sojin Nijeriya ne bayan kammala Makarantar sojin Royal Military Academy, Sandhurst. Ya zama Birgediya Janar a shekarar 1971, yana da shekaru 33, ya zama daya daga cikin manyan hafsoshin sojan Nijeriya.
Leadership ta ruwaito cewa a ranar 13 ga Fabrairun 1976, Janar Muhammed akan hanyarsa da ya saba bi a titin George da ke kusa da Sakatariyar gwamnatin tarayya a Ikoyi Legas, da misalin karfe 8 na safe, acikin motarsa kirar Mercedes-Benz, sai ga wasu gungun sojoji wadanda suka yi yunkurin juyin mulki karkashin jagorancin Laftanar Kanar Buka Suka Dimka, suka fito daga wani gidan mai, suka yi wa motar kwanton bauna kan hanyarsa ta zuwa ofishinsa da ke Barracks Dodan, inda suka kashe shi.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya ci gaba da gudanar da mulki, wanda ya kammala shirin mika mulki ga farar hula ta hanyar mika mulki ga Shehu Shagari a ranar 1 ga Oktoban 1979.
Abubuwan da Janar Murtala ya aiwatar a tarihin Nijeriya, wasu bangare na yabawa matuka wasu kuma akasin hakan saboda yanayin Jagorancinsa.
A jagorancinsa ya yi amfani da karfin mulkin soji, tattalin arzikin kasa ya habaka, wanda ya kara inganta rayuwa a Nijeriya.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
