Connect with us

News

Ƴan Najeriya sun mayar wa ɗan Tinubu martani bayan ya ce ‘a yi haƙuri da halin ƙunci’

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

Ƴan Najeriya sun yi wa ɗan shugaban ƙasar Bola Ahmad Tinubu ca, bayan da ya buƙaci al’umma su ƙara haƙuri da mahaifinsa sanadiyyar halin da ƙasar ke ciki.

Al’umma a Najeriya na cikin ƙuncin rayuwa sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da taɓarɓarewar darajar kuɗin ƙasar, naira.

Advertisement

Wani Zaki Ya Kashe Mutumin Da Ya Yi Shekara Tara Yana Renonsa A Jami’ar Obafemi Awolowo (Oau) Da Ke Jihar Osun.

A wani saƙo da ya wallafa ta shafinsa na instagram, Seyi Tinubu ya ce “Ba abin jin daɗi ba ne yadda mutanen Najeriya ke shan wahala kan lamarin da ya kamata a ce an wuce batun shi tun a shekarar da ta gabata.

“Na so a ce babu waɗannan wahalhalu da ake sha.”

Advertisement

Ya ƙara da cewa “Sai dai wajibi ne mu jure domin jin daɗi a nan gaba.”

Bayan wanann saƙo da ya wallafa ne ƴan Najeriya da dama, musamman a shafukan sada zumunta suka mayar wa ɗan na shugaban ƙasa martani.

Advertisement

Shahararren mawaƙi da ake kira Charly Boy ya wallafa a shafinsa na X cewa “Seyi Tinubu na ɗaura agogon naira miliyan 350 yayin da yake ce wa ƴan Najeriya su jure wa wahalar da ake ciki, mun ji.”

A nasa martanin, tsohon mai magana da yawun shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, wato Reuben Abati, wanda ya wallafa a shafin X, cewa ya yi “Seyi na da ƙarfin halin da zai tsoma bakinsa a wannan batu? Yana tunanin wannan lamari ne na cikin iyali? Me ya sani game da juriya?”

Advertisement

 

Seyi na daga cikin ƴaƴan shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka fi janyo cece-ku-ce a ƙasar.

Advertisement

Ko a kwanakin baya shugaban na Najeriya ya buƙaci ɗan nasa da duk wani da ba a buƙata ba da su daina shiga babban zauren taro na fadar shugaban ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending