News
Jami’an Hukumar EFCC sun yi dirar mikiya a kasuwar Wapa dake Jihar Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rahotanni da muke samu yanzu haka jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun yi dirar mikiya a kasuwar musayar kudaden waje ta Wapa dake jihar kano.
Ana ganin da Samamen nasu ba zai rasa nasaba da yadda ake sake samun hauhawar farashin Dala a Kasuwancinsu fagge na Nigeria ba.
Hukumar DSS Ta Nemi NLC Ta Janye Zanga-Zangarta Kan Tsadar Rayuwa
Wakilin mu ya rawaito cewa lamarin ya faru a kan idon sa ya shaida mana cewa jami’an sun Kama wasu daga cikin yan kasuwar yayin da wasu kuma suka tsare.
Wani da jaridar kadaura24 ta zanta da shi wanda ya nemi a sakaye sunansa, jami’an sun shiga kasuwar ne cikin kayan gidan, Inda yace bayan jami’an EFCC akwai sauran hadarkar jami’an tsaro.
Details soon
