News
Gwamnati Ta Kafa Dokar Hana Amfani Da Mazubin ‘Take Away’
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A yau Litinin ne gwamnatin jihar Oyo ta haramta amfani da mazaunin Take Away wajen saka abinci.
Rahotanni sun bayyana cewa, majalisar dokokin jihar a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, 2024, ita ta buƙaci gwamnatin jihar da ta haramta amfani da mazubin wajen zuba abin ci.
An Bukaci Kwamitocin Rikon Kwarya na Kananan Hukumomi Su Bai Wa Harkar Lafiya Fifiko
Saboda haka Majalisar ta ƙaddamar da kwamitin tabbatar da hana amfani da shi don kiyaye dokokin kayan abin ci a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Oluwaserimi Ajetunmobi, ya ce matakin ya ɗauki wani ɓangare ne na kokarin gwamnati na kiyaye ka’idojin kiyaye abinci a jihar.
Advertisements
