Connect with us

News

An Bukaci Kwamitocin Rikon Kwarya na Kananan Hukumomi Su Bai Wa Harkar Lafiya Fifiko

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

An jaddada bukatar da ake da ita ta sabbin kwamatin rikon kwarya da aka rantsar a jihar Kano da su ba da kulawa sosai ga lafiyar al’umma a kananan hukumominsu.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi wannan kiran a jiya jim kadan bayan gudanar da zagayen aikin rigakafin cutar shan inna a kananan hukumomin Kiru da Bebeji.

Gwamnan Kano Ya Roki Shugaban Kasa Tinubu Ya Bude Boda A Shigo Da Kayan Abinci

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka 

Kwamishinan ya ce kiran ya zama wajibi bisa la’akari da muhimmancin da kiwon lafiya ke da shi a kowace al’umma, yana mai jaddada cewa idan ba a samu isasshiyar lafiya ba zuwa makaranta, aikin noma da sauransu ba za su taba samuwa ba.

 

Advertisement

Ya kuma bukace su da su tabbatar da cewa duk yaran da suka cancanta a fadin kananan hukumomi 44 sun samu cikakken rigakafin cutar shan inna domin ma’aikatar da sauran masu ruwa da tsaki suna kan gaba wajen ganin an samu gagarumar nasarar aikin.

 

Dakta Labaran ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake bai wa bangaren lafiya na jihar ta hanyar kawo sauyi na gaba daya, matakin da ya samar da sakamako mai kyau.

 

Kwamishinan ya bayyana jin dadinsa kan yadda aikin ke gudana cikin kwanciyar hankali da nasara, inda ya nuna farin cikinsa da yadda jama’a suka fito suka fito da yaran wuraren da aka tanana don rigakafin da sauran cibiyoyi baya ga hadin kan da ake ba masu allurar rigakafi gida-gida, inda ya yaba da cewa aikin da aka yi a Kiru da Bebeji ya samu nasarar da ba ta gaza kashi 80 cikin 100 ba.

 

Advertisement

Ya kuma bukaci jama’a da su kara kaimi wajen fito da dukkan yaran da suka cancanta musamman wadanda suka fito daga makwabtan jihohin da ke, inda ya ce yawancinsu an dade ba a yi musu allurar rigakafi a jihohinsu ba da hakan ke su kawo tare da yada cututtuka a jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending