News
Majalisar Dattawa Ta Amince Da Karin Albashin Alƙalai Sau Uku
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da wani ƙudirin doka da ke neman ninka albashin Alƙalin Alƙalai Olukayode Ariwoola da sauran manyan alƙalan ƙasar sau uku.
Ƙudirin dokar ya tsallake karatu na uku a zaman majalisar na ranar Laraba.
Daga Karshe Dai Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Biyan Tallafin Man Fetur
Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin shari’a da ‘yancin ɗan’adam da kuma harkokin sharia na majalisar, wanda shugaban sa Mohammed Monguno ya gabatar.
Ɗan majalisar ya ce “biyan wadataccen albashi ga ma’aikatan shari’a zai ba su damar mayar da hankali wajen gudanar da aikinsu ba tare da tunanin wani nauyi na daban ba”.
A cewarsa: “Ƙarin albashin zai inganta ƙwarewar aikin ma’aikatan shari’a, lamarin da kuma zai dawo da martabar ɓangaren shari’a a tsakanin jama’ar ƙasa.”
Ya kuma bayyana cewa an shigar da tanadin wannan ƙari na albashin ma’aikatan shari’a a cikin ƙaramin kasafin kuɗi na 2024.
