News
Kungiyar SERAP tayi Allah wadai da kashe N21b wajen Gina ma Kashim Shettima gida
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙungiyar SERAP mai Fafutukar Yaƙi da cin Hanci a Najeriya da wasu ‘yan Najeriya sun nuna bacin ransu kan yadda aka kashe Naira Biliyan 21 don gina gidan Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki.
An kaddamar da sabon gidan mataimakin Shugaban kasa da ke kusa da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ranar Juma’a, inda gidan ya ƙunshi ofishin uwargidan Mataimakin Shugaban ƙasa, da Masallaci, da wuraren shakatawa da dai sauransu.
A cewar SERAP “Kashe Naira biliyan 21 a kan ginin gidan Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima almubazzaranci ne, kuma wannan ne ya ƙara tabbatar da cewa Gwamnatin Tinubu ba abinda ya dace tayi ba ne ake yi.
Sauran ‘yan Najeriya da suka mayar da martani ga wannan al’amari dai sun ce, kamata ya yi Gwamnati ta yi amfani da kudaden da aka kashe wajen aikin ceto miliyoyin ‘yan kasar daga matsalolin da suke fama da su na wahalhalun Rayuwa.
Wasu kuma sun nuna damuwa cewa an hana ‘yan jarida shiga wurin a lokacin da manyan Jami’an Gwamnati suka tafi rangadin a yayin kaddamar da aikin ranar Juma’a a Abuja.
SERAP a nata martanin ta cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a ranar Lahadi, ta ce, “A halin da ake ciki na talauci da ke kara ta’azzara, da basussukan da kasa ta ciyo, da kasa biyan mafi karancin albashin ma’aikata, kashe wannan maƙudan kuɗaɗe wajen gina gida almubazzaranci ne, kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa. Sannan ga Jami’an Gwamnati hakan ya saɓa ma rantsuwar kama aiki da suka yi.
Ya ci gaba da cewa, “Kudaden da aka kashe kan gina gidan zama na Mataimakin Shugaban ƙasa zai fi kyau a kashe su wajen samar da ababen more rayuwa da ake bukata domin bunkasar tattalin arziki, da magance kalubalen yara sama da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta, da kuma matsalar rashin tsaro da ta addabi kusan dukkanin sassan kasar nan.
Tun a ranar Juma’ar da aka ƙaddamar da gidan, an ta yin tsokaci kan rahotannin da ke cewa an hana kafafen yada labarai zagaya gidan tare da wasu mutanen da suka halarci kaddamar da aikin.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce mai gudanar da bikin kaddamar da aikin Eugenia Abu ya bayyana sunayen Baƙi na musamman da aka ba izinin shiga ginin.
