Connect with us

News

Yan Nijeriya na ci gaba da martani kan kashe Naira bilyan 21 don gina sabon gidan da mataimakin shugaban kasa zai zauna

Published

on

‘Yan Nijeriya na ci gaba da martani kan kashe Naira bilyan 21 don gina sabon gidan da mataimakin shugaban kasa zai zauna.

Wikki Times ta ruwaito cewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya kaddamar da bude sabon muhallin mataimakin shugaban kasa da aka kashe biliyan N21 wajen gina shi a birnin tarayya, Abuja.

Advertisement

Gwamnatin El-rufai Tafi Ko Wacce Gwamnati Sata A Tarihin Jihar Kaduna —Shehu Sani

Yayin bikin bude katafaren gidan, wanda aka yi ranar Juma’a, 7 ga watan Yuni, Tinubu ya bayyana cewa an gina gidan ne saboda kima da darajar ofishin mataimakin shugaban kasa ba kawai don Kwalliya ba.

Gidan, Wanda kamfanin Julis Berger ya gina, an fara bayar da kwangilar aikinsa shekaru 14 da suka gabata.

Advertisement

Tinubu, wanda mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya bayyana kudirin gwamnatinsa na yin komai a bayyane tare da yin tsantseni wajen sarrafa dukiyar kasa.

Shettima ya jinjinawa Tinubu bisa jajircewar sa wajen ganin an kammala aikin ginin gidan Wanda gwamnatocin baya suka gaza kammalawa saboda kalubale daban-daban da aikin ya fuskanta.

Advertisement

Kazalika, ya jinjinawa gwamnatin birnin tarayya, Abuja, bisa daukar nauyin kammala aikin domin kawo karshen asarar kudaden gwamnati.

An fara bayar da kwangilar aikin ginin gidan a shekarar 2010 akan kudi Naira biliyan N7 amma aka yi watsi da aikin a shekarar 2015, kamar yadda ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending