Connect with us

News

Wani Direba Ya Murkushe Mutum Shida Har Lahira Tare Da Raunata Mutum Bakwai A Jigawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wani direban canter mai shekaru 45 mai suna Tasi’u Ashiru ya murkushe mutane shida har lahira tare da raunata wasu bakwai a jihar Jigawa.

Advertisement

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa Jaridar DAILY POST cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba a Sabon Garin Takanebu, cikin karamar hukumar Miga, daura da hanyar Jahun zuwa Gujungu, inda direban ya rasa yadda zai yi da motar , inda ya ci karo da ‘yan kasuwa.

Hukumar NCDC Ta Sanar Da Mutuwar Mutane 30 Sakamakon Cutar Cholera A Sassan Najeriya

Da yawa sun mutu, yayin da wasu suka samu raunuka daban-daban.

Advertisement

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatarwa da Jaridar DAILY POST faruwar lamarin.

A cewarsa, “A ranar 12 ga watan Yuni, 2024, da misalin karfe 08:00 na safe, an samu mummunan hatsarin mota a Sabon Garin Takanebu, karamar hukumar Miga, tare da hanyar Jahun zuwa Gujungu, wanda ya hada da wata mota mai lamba Reg no. XA 519 KUR Mitsubishi Canter a karkashin da direbanta Tasi’u Ashiru mai shekaru 45 a kauyen Kara, karamar hukumar Ajingi, jihar Kano.”

Advertisement

“Da isa kasuwar Sabon Gari, direban ya rasa yadda zai yi, ya ci karo da ‘yan kasuwar, a sakamakon haka mutane goma (10) suka samu raunuka daban-daban yayin da uku (3) suka mutu nan take.”

DSP Shiisu ya ce tawagar ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka kai gawarwakin da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Jahun.

Advertisement

Ya kara da cewa karin mutane uku sun mutu a kan hanyarsu ta zuwa asibiti, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa shida.

Likitan da aka kira waya ya tabbatar da mutuwar wadanda lamarin ya rutsa da su, yayin da sauran bakwai da suka jikkata a halin yanzu suna kan karbar magani.

Advertisement

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, CP AT Abdullahi, ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending