News
Hukumar NCDC Ta Sanar Da Mutuwar Mutane 30 Sakamakon Cutar Cholera A Sassan Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar yaki da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta tabbatar da ɓarkewar annobar cutar Cholera ko kuma amai da gudawa a sassan Najeriya
Haka zalika rahotanni na nuni da cewa aƙalla mutum 65 da suka harbu da cutar ciki har da wasu 30 da suka mutu, daga watan janairun shekarar nan zuwa Yuni a ƙananan hukumomi 96 daga jihohi 30.
A cewar hukumar wajibi ne jama’ar ƙasar su ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan cuta da ke ci gaba da yaɗuwa a sassan Najeriyar.
Jami’in Dan Sanda Ya Harbe Alƙali Ana Tsaka Da Shari’ A Kotu
Hukumar ta NCDC ta ce ko a baya-bayan nan mutane 60 aka kwantar a asibitocin jihar Lagos bayan harbuwa da cutar ta Cholera ko kuma amai da gudawa, ciki har da 5 da suka mutu cikin ƙasa da sa’o’i 48.
NCDC ta bayyana cewa lura da yadda lokacin damuna ke ci gaba da ƙaratowa, wanda bisa al’ada ake ganin yawaitar masu harbuwa da wannan cuta sakamakon yadda ruwa kan koro tarin dattin da suka maƙale, dole ne jama’a su kula wajen tsaftar muhalli.
A cewar NCDC cikin shekarar nan ƙadai mutane dubu 1 da 141 suka nuna alamun harbuwa da Cholera wadda ta fi tsananta a jihohin Najeriyar 10.
