Connect with us

News

Muna bi tsarin da ya dace wajen ɗaukar Sabbin Jami’an ƴan Sanda 10,000 bisa cancanta – PSC

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Hukumar kula da ayyukan ‘yan Sanda ta kasa PSC a ranar Juma’a ta ce ɗaukar sabbin jami’an ‘yan Sanda 10,000 da za ayi, ana yin shi ne bisa tsarin da ya dace domin tabbatar da dukkanin su sun samu cikakkiyar chanchantar kama aiki.

Advertisement

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar Ikechukwu Ani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ya ce hukumar ta PSC ta sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa tun bayan kammalawa tare da fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasarar samun gurbin aiki a matsayin ‘yan Sanda a Najeriya.

Yawan Fama Da Zazzabin Cizon Sauro Na Haddasa Hawan Jini Da Ciwon Zuciya —Bincike

A cewar sanarwar “Hukumar ta damu matuka kan yadda ake cin zarafin kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke wanda ya ba ta ikon daukar waɗanda suka cancanta a aikin.

Advertisement

Yana da mahimmanci a bayyana cewa an bi tsarin da ya dace a duk lokacin da ake gudanar da tantancewar, kuma hukumar na son tabbatar da haƙƙinta na samun cikakken ikon daukar ma’aikata a rundunar ‘yan Sandan Najeriya.

Abin takaici ne yadda wasu jami’an ‘yan Sanda suke danganta gazawar hukumar a fili na gaza ɗaukar Jami’an da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu daga ‘yan fashi da ta’addanci,” inji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending