Connect with us

News

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar Da Harin ‘Yan Bindiga A Jihar Yobe

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai harin Yan bindiga a ƙauyen Mafa a ƙaramar Hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe, inda suka kashe mutanen da har yanzu ba a san yawansu ba.

Advertisement

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa, maharan sun yi sace-sace da yawa tare da banka wa shaguna da gidaje wuta a ƙauyen.

Wata Gobara Ta Tashi A Gidan Gwamnatin Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin Kakakinta Dungus Abdulkarim ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin.

Advertisement

“Har yanzu muna aiki ne domin tabbatar da adadin mutanen da suka rasu dalilin wannan harin, wanda aka kai a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 4 na yamma.

“Wasu mutane da ake kira Babagana Goni da Bako Ibrahim ne suka shigar da ƙorafi kan harin a ofishin ‘yan sanda da ke Tarmuwa, kuma dukansu mazauna yankin Mafa ne.

Advertisement

“Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne ɗauke da makamai sun kai hari yankin Mafa a kan babura su sama da 50 kuma sun cinna wa shaguna da gidaje da yawa wuta.

Maharan sun kashe mutane da dama, amma har yanzu ba mu ƙididdige adadin waɗanda harin ya shafa ba,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Advertisement

Ya ce bayan sun gama kai harin sun bar wasu makamai da rubutun larabci a jikinsu.

A ranar Juma’a NAN ya rawaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata makaranta da ke kusa da garin Geidam tare da kashe ɗalibai uku da jikkata ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending