News
Wata Gobara Ta Tashi A Gidan Gwamnatin Katsina
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar yau ta kone wani wuri a gidan gwamnatin Katsina.
Jaridar DAILY TRUST ta ruwaito cewa wurin da Gobara ta tashi yana hade da ofishin gwamna, inda ya ke ganawa da muhimman mutane.
Akwai Yiwuwar Ƙara Farashin Man Fetur A Najeriya A Hukumance
Har zuwa wannan lokaci ba a tabbatar da musabbabin tashin gobara ba, inda kuma ba a kayyade irin barnar da tayi ba.
Daily Trust ta rawaito cewa Gwamna Dikko Umaru Radda na a garin Funtuwa yana halartar taron shiyar domin tattaunawa da al’umomin da ke yankin kan halin da suke ciki
Advertisements
