Connect with us

News

Zamu Tabbatar An Yiwa Iyayen Yarinyar Da Aka Yi Wa Fyaɗe Ta Rasu Adalci —Gwamnatin Kano

Published

on

images (1)

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Ma’aikatar kula da harkokin mata da yara da kuma masu buƙata  ta musamman a jihar Kano ta ce za ta tabbatar an yiwa iyayen yarinyar nan da aka yi wa fyaɗe ta rasu adalci.

Advertisement

Ana zargin wani mai kyamis da yiwa wata yarinya ‘yar shekara 9 fyade a lokacin da ta ke zazzabi aka kaita a duba ta, al’amarin da yayi sanadin mutuwarta, abinda yasa gwamnati ta ce ba za zuba ido maganar ta tafi a haka ba.

Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba

Cikin wata sanarwa da kwamishinaniyar ma’aikatar kula da harkokin mata da ƙananan yara, Hajiya Aisha Lawan Saji ta fitar, ta ce dole ne su wuce gaba a yi adalci ga wannan ƴar ƙaramar yarinyar da ta rasa ranta saboda ɗabi’ar dabbobi da wannan mutum ya nuna.

Advertisement

Mahaifin yarinyar Sadiq Badamasi ya shaida BBC cewa lamarin ya auku ne lokacin da ya kai ‘ya’yansa mata biyu da namiji daya, kyamis a duba su saboda suna zazzabi, a unguwar Jaba a birnin Kano.

Malam Sadiq ya ce mai kyamis ɗin ya ce mazan biyu za a yi masu allura yayin da ita kuma yarinyar za a ƙara mata ruwa, “bayan na koma sai na tarar an ƙara mata ruwan abun da yake faɗa kenan, da rigar a hannu ya aje ta a gefen benci, sai ta ce mani Abba ciwo ƙuguna da cinyata ko ina yana ciwo.”

Advertisement

“Mun kawo ta gida, bayan wani lokaci kuma sai ta sake galabaicewa,ta riƙa zubar da jini sosai,bayan mun sanar da mai kyamis sai ya ce aje ayi mata hoto” cewar malam Sadiq

Sadiq Badamasi yace sun tafi zuwa wurin yi mata hoton , sai yaji bai gamsu ba, don haka ya tafi asibitin gwamnati.

Advertisement

“Sun duba ta asibitin Murtala suka kuma tabbatar cewa fyaɗe aka yi mata gaba da baya, abu mummuna wanda ya ƙazanta sosai, saboda idan aka ɗaga yarinyar kana hango kayan cikin ta duɓurarta da kuam gabanta, bayan wani lokaci sai Allah ya yi mata rasuwa.”

Kuma ko da aka bibiyi lamarin, sai aka fahimci cewa mai kyamis din da ya duba ta ake zargi da auka mata, inda aka kama shi. Kuma tuni aka gurfanar da shi a gaban kotu.

Advertisement

Barrista Badamasi Sulaiman Gandu shi ne lauyan iyayen marigayiyar, ya kuma shaida wa BBC cewa an tuhumi mai kyamis din da laifin fyaɗe da kuma kisan kai, “Ya musanta duka zarge-zargen, kuma kotu ta tura shi gidan gyaran hali zuwa ranar 30 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraren shari’ar.”

Matsalar fyaɗe ta jima tana ciwa al’umma tuwo a ƙwarya a Najeriya kuma fyaden bai tsaya a kan manya ba ko ƴan mata, galibi a wannan zamanin an fi cin zarafin ƙananan yara da jarirai.

Advertisement

Kuma da dama basa fitowa su sanar da hukumomi saboda tsoron tsangwama, abinda ake ganin yin hakan kuskure ne.

Wasu dai na ganin rashin hukunta waɗanda aka samu da laifin fyaɗe ne yake sanya al’amarin ƙara ta’azzara, a gefe guda kuma akwai masu kiraye-kirayen da a tsaurara dokokin hukunta wadanda aka samu da laifin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending