News
Wasu Yan Daba Sun Cinnawa Ofishin Yan Bijilanti Wuta A Jihar Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu da ake zargin Yan Daba ne sun afkawa wani ofishin yan Bijilanti dake unguwar Arewa Dake Kofar Mazugal a Karamar Hukumar Dala a jihar Kano
Rahotanni na nuni da cewa bata garin sun farwa ofishin yan Bijilanti ne da dadre kuma nan take suka farwa ofishin tare da cinna masa wuta wanda hakan yayi sanadiyar kone wasu muhimman bayanai da kuma kayan dake cinkinsa
Zamu Tabbatar An Yiwa Iyayen Yarinyar Da Aka Yi Wa Fyaɗe Ta Rasu Adalci —Gwamnatin Kano
Haka zalika bata garin matasan sunyi amfani da muggan makamai Wajen Zuwa ofishin tare da barazana hallaka wani mutum da suka samu a wajen idan bai basu hadin kai wajen abinda suka kuduri aniyar yi ba.
Wani rangadi da Mikiya Hausa Time ta kai ofishin ta gano yadda bata garin suka lalata dukkan kayan dake cinkinsa ta hanyar konesu,tare da awon gaba da kayan sawa wato Uniform da kayan aiki da Sauran Muhimman abubuwa Dake cinkinsa .
Rahotanni na nuni da cewa Bata garin sun dauki wanann mataki ne saboda yadda jami’an Bijilanti din suka hana su sakat wajen sace sace a yankin
Wanda ake kallon hakan yasa sukayi gangami domin daukar matakin dakile yunkurin ayyukan Yan Bijilanti din Dake Yankin
A nasa bangaren Kwamandan Dake Kula da Ofishin Bijilanti din Mai Suna Abdullahi Hussain ya bayyana takaicinsa da wanann lamari sai dai yace hakan ba Zai Kashe Musu Guiwa ba, Wajen Cigaba da fatattakar batagraua Yankin ba.
Abdullahi Hussain ya Kuma bukaci Masu ruwa da tsaki da su Kawo musu Dauki Wajen Gyara Ofishin Sakamakon lalacewa da yayi Domin Cigaba da ayyukan su na dakile ayyukan Batagari a Yankin
