News
Bitar Wayar Dakai Kan Sabbin Dabarun Ayyuka Da Shirin DRF Ya Shiryawa Mambobin SCHSS Don Cigaban Kiwon Lafiya
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Bitar Wayar Dakai Kan Sabbin Dabarun Ayyuka Da Shirin Samar Da Magunguna Ta Shirya Kan Masu Hannun Jari Don Cigaban Lafiya
Manufar gudanar da bitar taron shine ganin duka masu zuba hannun jari a kungiyar sunbi sabbin tsarukan da aka gindaya wanda Hukumar dake samar da kayayyakin lafiya masu dorewa ta shirya na tsahon kwana uku domin wayarwa da dukkannin mambobinta baki daya a dukkanin kanana da manyan asibitocin Jihar kano baki daya.
An Cafke Matashi Sanye Da Kayan Mata A Wani Babban Kantin Sayayya A Kano.
Haka zalika nadaga cikin makasudin taron wajen ganin masu hannun jarin sunbi duk hanyoyin daya dace wajen ganin sunci da harkar inganta samar da magunguna ta jihar kano gaba, musan idan aka tsaya akan sharrudan aka gindaya wajen gudanar da aiki bisa ka’ida da gaskiya da rukon amana kamar yadda doka ta tanadar.
An Cafke Matashi Sanye Da Kayan Mata A Wani Babban Kantin Sayayya A Kano.
A yayin jawabin chairman kuma babban darakta na Kungiyar magunguna ta Hukumar lafiya ta Jihar Kano Kamilu Mudi Salisu ya tunatar da masu hannun jari yadda sabbin tsarukan zasu kasance domin samun abunda ake da bukata wajen inganta harkokin lafiya a fadin Jihar kano baki daya.
Yakara dacewa, dukannin mambobin zasuyi aiki tukuru akan abin dake cikin kundin dokokin tsarin gudanar da ayyuka na yau da kullum wanda ya ayyana bin kalma bayan kalma domin ganin amfahimci duk yadda za’a warware ko wace irin matsala da aka tunkara yayin gudanar da aiki na yau da kullum na tsaftace harkar samar da magunguna masu dorewa a fadin jihar Kano baki daya.
Kamilu yakara da cewa nadaga cikin matsalolin da suke fuskanta shine idan an samar da wasu sabbin tsaruka haka ake ajiye kundin ba tare da bibiyar ba wanda hakan yazama al’ada ga mambobin wanda hakan ke janyo asara da kalubale da yawa akan harkar cigaban inganta lafiya.
Daga bisani yaja kunnen al’umma tare da gargadi akan kowa yayi amfani da abinda aka tattauna a taron bitar wayar da kai wanda hakan zai zama gagarumar nasara a fannin samar da magunguna dama inganta lafiyar baki daya a fadin Jihar ta kanon dabo.
A karshe ya yabawa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf wajen ganin bawa harkar lafiya muhimmanci tundaga lokacin dayazama zababben Gwamnan Jihar kano wanda ko yanzu ance kwalliya ta biya kudin sabulu a cikin mulkinsa na takaitaccen wa’adi musamman idan akayi la’akari da manyan ayyukan da Hukumar lafiya ta Jihar kano ta gudanar karkasin jagorancin mai gayya mai aiki Dr Labaran Yusuf wanda yayi alkawarin samar da wasu sabbin muhamman aiyuka a harkar lafiya a fadin jihar..
Wasu daga cikin malarta taron sun tofa albarkacin bakinsu wanda ya hada da Tukur Ibrahim, Nura Yahaya da kuma Bello Muhammad a matsayinsu na jagorori a tafiyar inda suka ayyana bin sabbin ka’idojin da aka gindaya shine mafi A’ala harkar bunkasa harkokin samar da magunguna masu derewa a manya da kananan asibitocin dake fadin Jihar kano baki daya
