News
Akalla Mutane 33 Sun Mutu A Wani Wurin Hakar Ma’adanai A Birnin Tehran
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata fashewa da ta abku a wani wurin hakar ma’adanai a gabashin Iran ta kashe akalla ma’aikata 33 tare da jikkata wasu 17, cewar jami’ai a yau Lahadi, lamarin na farko mafi muni a harkar hakar ma’adanai a tarihin kasar, inda ba a ma ga wasu ma’aikatan ba, sa’oi bayan afkuwar lamarin.
Fashewar ta abku ne a wurin hakar ma’adani dake garin Tabas, mai nisan kilomita 540, kudu maso gabashin babban birnin kasar Tehran, a daren jiya Asabar. Ya zuwa safiyar Lahadin nan, abokan aiki da iyalai da yan’uwa sun kasance cikin kuka da jimami a lokacin da motoci suka zo da gawawwakin abokan aikin su lullube da kura.
Faduwar Darajar Naira Da Tsadar Man Fetur Ke Ruruta Tsadar Abubuwa A Najeriya
Kimanin mutane 70 ne ke bakin aiki a lokacin da fashewar ta afku. Daga bisani, kafar talabijin ta kasar tace, ana kyautata zaton mutum 17 daga ciki na datse, a karkashin kasa da zurfin mita 200, kimanin kafa 650. To sai dai alkalumman na cigaba da sauyawa ya zuwa ranar Lahadin nan, dangane da bala’in da ya faru a yankin na karkara, inda wasu rahotannin ke cewa, adadin wadanda suka mutu yafi adadin da aka bayyanawa.
Hukumomi sun dora alhakin fashewar kan wani gas dake yoyo. Ana dai yawan samun irin wannan gas din a wuraren da ake hakar ma’adanai, duk da dai matakan samar da kariya na zamani sun nemi a rika samar da hanyoyin samun iska da sauran matakan kare ma’aikata.
A nan take dai ba a iya gane irin matakan kariya da ke akwai a kamfanin mai zaman kan shi ba na Mandanjoo dake kula da wurin hakar ma’adanai na Tabas Parvadeh. Kokarin da aka yi na jin ta bakin kamfanin a ranar Lahadi ya ci tura.
Sabon shugaban kasar ta Parisa, wato Iran, Masoud Pezeshkian da ke shirye shiryen zuwa birnin New York na Amurka domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, ya ce, ya bayar da umurnin yin duk mai yuwuwa na ganin an ceto wadanda su ka makale, tare da tallafawa iyalan su. Ya kara da cewa, tuni har an soma gudanar da bincike kan afkuwar lamarin.
