Connect with us

News

Kotu Ta Tabbatar Da Alhaji Mustapha Jokolo A Matsayin Sarkin Gwandu

Published

on

Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Tarayya Yin Titin Jirgin Kasa A Filin Jama'a A Kuyan Ta Inna

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Ƙotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta ce Alhaji Mustapha Haruna Jokolo ne sarkin Gwandu da ke Jihar Kebbi, saboda a cewarta ba a bi ƙa’ida ba wajen sauke shi daga sarautar da aka yi.

Advertisement

Alkalin kotun da ke zama a Sokoto Ibiowei Tobi, ya sake tabbatar da hukuncin da babbar kotun jihar Kebbi ta yi cewar gwamnatin jihar ta wancan lokaci ta saba ka’ida wajen matakan da ta ɗauka na sauke Sarkin Gwandu na 14 daga karagar mulki.

Aƙalla Mutum Bakwai Ne Suka Rasu Sakamakon Ruhsewar Gini A Abuja

Saboda haka kotu ta yi watsi da ƙarar da gwamnatin jihar Kebbi ta gabatar a gaban ta, domin neman halarta matakan da ta bi wajen sauke sarkin.

Advertisement

Da wannan hukunci yanzu kallo ya koma kotun ƙoli wadda ake saran ta yanke hukunci na ƙarshe dangane da wannan shari’a, da aka kwashe sama da shekaru 20 ana tafkawa.

 

Advertisement

AFP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending