Connect with us

News

Kotu Ta Dakatar Da VIO Daga Cin Tarar Masu Ababen Hawa

Published

on

Kotu ta dakatar da hukumar VIO daga cin tarar masu ababen hawa a Najeriya
Kotu ta haramtawa VIO daga kamawa ko kuma cin tarar masu ababen hawa a Najeriya.

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta haramtawa Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa ta VIO, ta daina kamawa da kuna  kwacewa ko kuma cin tarar masu ababen hawa.

Advertisement

Haka nan kotun ta umarci jami’an hukumar na VIO su daina tsaida masu ababen hawa akan hanyoyin ƙasar.

Akalla Mutane 350 Suka Kamu Da Cutar Daji A Jihar Katsina

Mai shari’a Evelyn Maha ce dai ta yanke wannan hukuncin, bayan da Abubakar Marshal, mai rajin kare hakkin bil’adama ya shigar da ƙara kan lamarin.

Advertisement

A hukuncin nata ta ce, kotun ta gamsu da hujjojin mai ƙara na cewa babu wata doka da ta baiwa waɗanda ake ƙara hurumin tsaidawa da kamawa da kwacewa ko kuma cin tarar masu ababen hawa a kan hanya.

Mai shari’a Maha ta kuma bada umarnin dakatar da waɗanda ake ƙara, daga tauye haƙƙin ƴan Najeriya na yin zirga-zirga yadda suke suke so ba tare da sahalewar doka ba.

Advertisement

 

FRI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending