Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Aika Wa Majalisun Dokoki Dokar Sake Fasalin Haraji A Najeriya

Published

on

Shugaba Tinubu ya aika wa Majalisun Dokaki Daftarin Sake Fasalin Haraji a Najeriya
Advertisements
Advertisements
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya aike wa da majalisun Dokokin Najeriya daftarin dokar gyaran haraji.

Shugaba Tinubu wanda a yanzu haka ke ƙasar Ingila, ya aike da wasiƙar ne zuwa ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, wacce kuma ya karanta ta a yayin zaman majalisar da aka yi a Ranar Alhamis.

Advertisement

Kotu Ta Dakatar Da VIO Daga Cin Tarar Masu Ababen Hawa

Shi ma takwaransa na majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta wannan wannan wasiƙa ta shugaban ƙasa zauren majalisar.

Bayan kammala karantawar, sai Akpabio ya miƙa wa kwamitin kuɗi na majalisar domin yin nazarinta tare da ba wa kwamitin makonni uku domin ba da rahoto a kai.

Daftarin dokokin sun ƙunshi Dokar Haraji ta 2024 wacce za ta ba da wani fasali na karɓar haraji a Najeriya da Dokar Kula da Haraji wacce za ta samar da fasali na doka ka dukkan nau’o’in Harajin Najeriya da magance kace-na-nace kan haraji.

Advertisement

Sauran daftarorin sun haɗa da Daftarin Samar Hukumar Kula da Haraji wacce za ta maye gurbin Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa. Sai kuma Daftarin Samar da Ma’aikatar Haraji ta Baiɗaya wacce za ta samar da Kotun Sauraron Karafe-ƙorafen Haraji.

Shugaba Tinubu ya ce ya gabatar da waɗannan daftarorin doka ne domin tallafa wa ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen inganta tattalin arziƙi.

“Waɗannan daftarorin Haraji sun dace da manufofin gwamnatina wajen kawo gyara ga tattalin arziƙi ta hanyar inganta biyan haraji da inganta hukumomin da abin ya shafa da tabbatar da tsarin harkar kuɗi ba tare da wata ƙumbiya-ƙumbiya ba,” a cewar shugaba Tinubu.

Advertisement

Shugaba Tinubu ya bayyana shirin gabatar da daftarorin ne tun a cikin jawabinsa na tunawa da ranar samun ‘yancin kan Najeriya, domin tun a bara shugaban ya kafa kwamitin da zai kawo gyara ga sha’anin kuɗin da haraji a ƙarƙashin jagorancin Taiwo Oyedele wanda aka ɗora wa alhakin zaƙulo hanyoyin da za su inganta hanyar tattara haraji da ba da rahoto na gaskiya kan haraji da tabbatar da amfani da harajin yadda ya kamata domin tabbatar da sahihancin harkar haraji da ƙarfafa guiwa wajen biyansa.

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending