News
Sanatocin Arewacin Najeriya 12 Da Suka Gaza Gabatar Da Ƙudiri A Watanni 15 — Rahoto
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD TUKUNTAWA
Wani bincike da Jaridar WIKKITIMES ta yi ya bayyana cewa sanatoci 12 daga jihohin arewacin Nijeriya ba su gabatar da kowanne ƙudiri ba a cikin watanni 15 na farkon wa’adin majalisar dokoki ta 10, wadda ta fara aiki tun ranar 13 ga Yuni, 2023.
Waɗannan sanatoci na wakiltar yankuna da ke fama da matsaloli masu tsanani irin su rashin tsaro, talauci, rashin ingantaccen ababen more rayuwa, da rashin aikin yi.
Shugaba Tinubu Ya Aika Wa Majalisun Dokoki Dokar Sake Fasalin Haraji A Najeriya
Daga cikin Sanatocin da ba su gabatar da ƙudiri ba akwai Abdul Ningi (Bauchi ta tsakiya), Musa Mustapha (Yobe ta Gabas), da Ahmed Lawan (Yobe ta Arewa), wanda shi ne tsohon Shugaban Majalisar Dattawa.
Wasu sanatocin kuma sun fito daga jihohin Adamawa, Taraba, Sokoto, da Filato, waɗanda duk suna fama da manyan matsalolin tattalin arziki da zamantakewa.
Duk da matsalolin da ke addabar waɗannan yankuna — kamar rashin ingantaccen kiwon lafiya, ilimi, da ababen cigaban rayuwa — wadannan sanatoci ba su ɗauki matakin samar da doka ba don magance wadannan matsaloli masu tsanani.
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa masana sun yi Allah wadai da rashin wannan aiki na ƴan majalisar, suna kallon hakan a matsayin gazawar wakiltar muradun al’ummominsu da kuma ɗumama kujera.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion5 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
