Connect with us

News

Barau Jibrin, Ndume Da Sanatoci 38 Ka Iya Rasa Kujerun Su Saboda Karɓar Alawus A Majalisu Biyu

Published

on

DAGA  MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Sanatoci aƙalla 40 ne ka iya rasa kujerar su, saboda kasancewar su mambobi a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar ECOWAS ta Afrika ta Yamma, kuma duk suke karɓar alawus-alawus daga majalisun biyu, abin da ya karya doka.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito  wasu daga cikin waɗanda tsigewar ka iya shafa sun haɗa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda a yanzu haka shi ne Kakakin Majalisar ECOWAS na Riƙon, Ali Ndume, Abiodun Olujimi, Smart Adeyemi, Tolu Odebiyi da Mshelia Haruna, da kuma wasu da dama.

Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC A Gundumar Galadima Ta Kori Shugaban Jam’iyyar Na Jihar Alh Tukur Danfulani

Lamarin ya taso ne daga wata ƙara da Kungiyar Bin Diddigin ‘Yan Majalisa (ALDRAP) ta shigar a gaban Babbar Kotun Najeriya, Abuja, inda ƙungiyar ya maka ‘yan majalisar kotu.

Advertisement

ALDRAP dai tun kafin ta je kotu, sai da ta fara yin kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio cewa ya ayyana kujerun sanatocin cewa ba su ne a kai ba, an tsige su, saboda sun shiga wata majalisa sun haɗa mamba ɗin majalisa biyu, wato ta Najeriya da ta ECOWAS, kuma duk ana biyan su a majalisun biyu.

Yayin da suka ga Akpabio bai yi komai ba, sai ALDRAP ta aika masa da takardar gargaɗi, cewa za su ɗauki matakin shari’a.

Advertisement

A cikin wasiƙar da suka aika a ranar 8 ga Afrilu, mai ɗauke da sa hannun Sakataren ALDRAP, Tonye Clinton Jaja, ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa, “Idan Majalisa ba ta ɗauki mataki a cikin kwanaki bakwai ba, to za ta garzaya kotu.

Sun jaddada cewa dokar Najeriya Sashe na 68(1) na Kundin Dokokin 1999, ya haramta wa sanata ya zama mamba na Majalisar ECOWAS. Kuma ita ma Dokar 2017 ta ECOWAS ta Sashe na 18 ya yi hani da zama mamba a majalisa biyu.

Advertisement

 

Sun ce ita ma ECOWAS ta haramta ɗan majalisa ya zama mamba a wuri biyu, kamar yadda ta haramta masa karɓar alawus-alawus a majalisa biyu.

Advertisement

 

ALDRAP ta roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta jaddada dokar shiga Majalisar ECOWAS, wato inda doka ta ce, duk mai sha’awar zama mamba a Majalisar ECOWAS ko ta Afirka, to tilas sai ya fara yin murabus, ya sauka daga kujerar sa a Majalisar Dattawa.

Advertisement

Sun kuma roƙi kotu ta dakatar da biyan sanatocin su 40 dukkan albashin su da alawus-alawus ɗin da Majalisar Dattawa ke biyan su, saboda kwanan nan aka ƙaddamar da su mambobin ECOWAS, wasu kuma mambobin Majalisar Afrika.”

ALDRAP ta kuma roƙi kotu ta bai wa INEC umarnin shirya zaɓukan cike-gurbi a yankunan sanatocin su 40, domin a zaɓi waɗanda za su maye gurbin su a Majalisar Dattawa, a cikin kwanaki 30.

Advertisement

A ranar 4 ga Afrilu ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da Majalisar ECOWAS ta Shida, bayan cikar wa’adin ta Biyar a ranar 8 ga Maris, 2024

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending