News
Wani Jirgin Sama Ya Kuma Tsallake Rijiya Da Baya A Filin Jirgin Saman Legas
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jirgin mai dauke da fasinjoji 52 da ma’aikatan jirgi da ya taso ne daga filin jirgin Abuja
A cewar majiyoyin da ke filin jirgin, an rufe titin jirgin sama mai lamba 18 na hagu da zirga-zirgar jiragen sama yayin da jami’an hukumar ceto da kashe gobara ta Aerodrome na hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) suka yi tattaki zuwa wurin da lamarin ya faru domin ceto fasinjojin.
Barau Jibrin, Ndume Da Sanatoci 38 Ka Iya Rasa Kujerun Su Saboda Karɓar Alawus A Majalisu Biyu
The Nation ta ruwaito cewa Xejet Airlines jirgin sama ne kawai na kasuwanci a Najeriya.
Jirgin dai yana aiki ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas (LOS).
Majiyar ta yi nuni da cewa: “Wani jirgin sama mallakar kamfanin jiragen sama na Xejet ya zarce daga titin jirgin a filin jirgin saman Legas. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:29 na safe, yayin da jirgin ya kutsa cikin gabar ciyawa ta B5.
“Jirgin na dauke da alamar rajista – 5NBZZ, Embraer 145 yana dauke da fasinjoji 52 tare da ma’aikatansa uku.
” Jami’an kashe gobara da ceto suna nan a kasa don taimakawa wajen kwashe fasinjojin.
“A halin yanzu Runway18L yana rufe
Masana sun ce jirgin sama ya tashi daga kan titin jirgin, ana iya danganta shi da mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Asabar a Legas.”
