News
Sanatoci Sun Rabe Naira Miliyan 218 Kudin Shagalin Hutu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Biyo bayan kalaman shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio kan batun kuɗin hutun sanatoci, an tabbatar da cewa kowane sanata ya samu N2m a matsayin kuɗin alawus na zirga-zirga a lokacin hutun har zuwa watan Satumba, lokacin da za su dawo.
Kamar yadda Premium Times ta rahoto, alawus ɗin 2m na zirga-zirga su ne kuɗin da Akpabio yake maganar za a tura wa kowannen su a yayin zaman majalisar na ranar Litinin, 7 ga watan Agusta.
Da yake tabbatar da hakan, wani sanata wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an tura wa kowane sanata N2m bayan zaman majalisar na ranar Litinin.
Bayanai na cewa dukkanin sanatocin guda 109 na majalisar dattawa, N2m aka tura wa kowanen su wanda hakan ya sanya kuɗin sun kai jimillar N218m .
A ɗaya ɓangaren kuma, har yanzu ba a tabbatar da cewa ko Akpabio da sauran shugabannin majalisar N2m suka samu a matsayin kuɗin alawus ɗin hutun ba.
A bisa tsarin albashin da hukumar RMAFC ta amince da shi, albashin shugabannin majalisa ya fi na sauran sanatoci.
Shugabannin majalisar su ne, shugaban masu rinjaye, mataimakin shugaban masu rinjaye, babban mai tsawatarwa da mataimakin mai tsawatsarwa Sauran sun haɗa da shugaban marasa rinjaye, mataimakin shugaban marasa rinjaye, ƙaramin mai tsawatsarwa da mataimakin ƙaramin mai tsawatarwa.
A tsarin albashin da hukumar RMAFC ta amince da shi, sanata yana samun N2,026,400 sannan yana samun alawus na N202,240 a shekara.
A na shi ɓangaren, mataimakin shugaban majalisar dattawa yana samun albashin N2,309,166, da alawus N230,916.
