News
Ya Kamata Hukumar Hisba da ta gayyaci Sadiya Haruna da G Fresh akan wulakanta aure a sohiyal media—Amb Auwalu Muhd Danlarabawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Kungiyar Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation ta yi kira ga Hisba da ta gayyaci Sadiya Haruna da G Fresh Al’amin akan abubuwan da sukeyi na wulakanta aure a sohiyal media.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation Amb Auwalu Muhd Danlarabawa Yarabawa manema labarai.
Zamu tabbatar an yiwa kowa rigakafin cutar shan inna a jahar kano—Dr.Labaran
Muna kira ga Hukumar Hisba da ta gayyaci Sadiya Haruna da G Fresh Al’amin akan abubuwan da sukeyi na wulakanta aure a sohiyal media
Yakara da cewa ya kama ta Hukumar Hisba ta yi magnaa dan kare martabar aure kamar yanda Addinin muslunci ya tabada.
Duba ga yadda suke ta kalamai Marasa daraja da tozarci a Tsakanin su bayan Auren nasu ba wani dadewa yayi ba.