News
Zamu tabbatar an yiwa kowa rigakafin cutar shan inna a jahar kano—Dr.Labaran
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA.
A ci gaba da gudanar da aikin rigakafin cutar shan inna da ake gudanarwa a jihar kano, kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf a ranar Talata ya ziyarci kananan hukumomin Kabo da Shanono.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Jami’in yada labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya rabawa manema labarai.
Dr. Labaran yace wannan na daya daga cikin alkawuran da ya dauka dangane da samar da dukkan kayan aikin da ake bukata na aikin rigakafin cutar shan inna jahar kano .
Kwamishinan yace ya gamsu akan yadda aka yi isassun tsare-tsare a kananan hukumomin biyun kamar tura tawagogin ma’aikatan da aka aiwatar a kan lokaci zuwa cibiyoyin rigakafi.
Dakta Labaran wanda ya samu wakilcin Darakta Janar na Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya Masu Zaman Kansu (PHIMA), Farfesa Salisu Ibrahim Ahmad, ya koka da rashin adadin yara 61 da aka samu a karamar hukumar Shanono cikin kwanaki biyu da aka fara gudanar da aikin rigakafin cutar shan inna kashi na biyu.
A cewarsa, wannan wani lamari ne da ba a so a ce an samu a cikin ‘yan kwanaki kadan da ake gudanar da aikin rigakafin cutar shan inna , ya kara da cewa kananan hukumomi kamar Gwarzo, Bagwai, da dai sauransu har ma mutanen jihar Katsina suna zuwa domin samun kiwon lafiya.
Yakara da cewa duk da haka sunn ba da umarnin a zurfafa bincike akan lamarin