News
Kotu Ta Kwace Kujerar Dan Majalisar Tarayya Na Tarauni na NNPP ta Baiwa APC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar Kano Dake a Miller road ta kwace Kujerar Dan majalisar tarayya na karamar hukumar Tarauni Hon Muktari Yarima na NNPP ta dawo da ita hannun Hon Hafizu Kawu na Jami’iyar APC.
Kotun mai alkalai uku, ta tabbatar da Hon Hafiz Ibrahim Kawu na Jam’iyyar APC amatsayin wanda ta mikawa kujerar bisa dogaro da hujjar gabatar da sakamakon bogi na Firamare da Danmajalisar Yarima yayi.
Yarima dai ya tsaya ne karkashin inuwar Jam’iyyar NNPP a zaben da akayi a watan Fabarerun daya gabata.
Jim kadan bayan fitowa daga kotun, lauyan Mukhtar Yarima Barista Rabiu Sadiq yace sun karbi wannan hukunci kuma zasu daukaka kara